18 Agusta 2020 - 10:26
​Zarif: Lokacin Iko Da Tinkaho Na Amurka A Duniya Ya Kawo Karshe

Ministan harkokin wajen kasar Iran Muhammad Jawad Zarif ya bayyana cewa, lokacin iko da tinkaho da girman kai na Amurka a duniya, ya kawo karshe.

ABNA24 : A lokacin da yake zantawa da tashar talabijin ta kasar Iran a daren jiya a birnin Tehran, Ministan harkokin wajen kasar ta Iran Muhammad Jawad Zarif ya bayyana cewa; lokacin da Amurka za ta rika yin iko da duniya yadda ta ga dama a lokutan baya, yanzu ya zo karshe.

Ya ce babban dalili kan hakan shi ne yadda dukkanin kasashen duniya suka juya wa Amurka baya a kwamitin tsaron majlaisar dinkin duniya, a lokacin da ta gabatar da daftrin kudirin da ke neman a sabunta takunkuman hana Iran saye da sayar da makamai, inda hatta abokan kawacenta kasashen turai, ba su goyi bayanta kan hakan ba, wanda shi ne irinsa na farko da ya faru a cikin shekaru 75 bayan kafa majalisar dinkin duniya.

Zarif ya ce yana da kyau gwamnatin ta Amurka ta zauna ta yi karatun ta-natsu dangane da siyasarta a kan kasashen duniya, tare da gyara kura-kuran da take tafkawa, biyo bayan wannan abin kunya da ya faru da ita a kwamitin tsaron majalisar dinkin duniya.

Dangane da batun shirin Iran na nukiliya kuwa, Zarif ya bayyana cewa, Iran tana ci gaba da gudanar da harkokinta kamar yadda ta sanar da hukumar makamashin nukiliya ta duniya IAEA, duk da cewa dai hukumar ta bukaci wasu bayanai daga Iran, inda zarif ya ce daga yanzu ba kowadanne irin bayanai hukumar za ta samu daga Iran ba, sai wadanda doka ta kasa da kasa ta yarje mata kawai, sakamakon yadda hukumar ta fara tasirantuwa da matsin lambar Amurka da wasu masu yi mata amshin shata.

342/